Samar da ingantaccen tsaro da kariya (Greater Access to defence and Justice) wani tsari ne da zai dauki tsawon watanni ashirin da hudu (24 months) ana gabatar da shi.
Wannan tsari zai kunshi samar da ofishin masu kare hakkokin al’umma (Public Defenders Office) a jihar kano.
Muradan Wannan Aikin
Muradan da ake fatan samun nasara a kansu sun hadar da;
1) Inganta hanyoyin samun tallafin shari’a ga ilahirin jama’ar kano ta hanyar samar da ofishin kare hakkokin al’umma a kano.
2) Samar da hanyoyin da za a yi wa lauyoyi kaimi da kuma karfafa musu gwiwa domin kare hakkokin
jama’a, musamman marasa galihu.
3) Samarwa da kuma inganta alaka tsakanin wannan kungiya da sauran kungiyoyin da ke da alaqa da fannin shari’a a jihar kano.
4) Kara wayar da kan al’umma domin su san yadda za su iya amfana daga wannan ofishin masu kare hakkokin al’umma wadda za a samar a jihar kano.
Leave a Comment